You are on page 1of 2

SCRIPT JINGLE OF MALARIA (ACT)

Warkar da zazzabin cizon sauro da maganin act: Abin da ya kamata ka sani.


1. Menene Zazzabin cizon sauro?
Zazzabin cizon sauro cuta ce dake yaduwa daga wannan mutum zuwa wancan
bayan mace sauro dake dauke da cutar ta cij mutum sannan kan sa shama jinni
a jikin mutum. Shama jinin kan kai hali ta kuma lalata ‘yan halittun jini wanda
hakan zai sa mutum ya kamu da rashihjn lafiya ya kuma nuna alamun kamuwa
da zazzabin cizon sauro. Duk muntumin daya bari sauro ya cije shi to ba
shakka yana tattare da hadarin kamuwa da zazzabin cizon sauro.
2. wadanne alamu ne ke nuna mutum ya kamu da zazzabin cizon sauro?
 Zazzabi/Zafin Jiki
 Jin Sanyi
 Kaduwar Jiki
 Rashin Sha’ar Abinci
 Dacin baki
 Lalaci
 Jiri
 Amai/Kumallo
 Dashewar idanu da tafin hannu
 Da kuma harshe.
3. gwaji da kuma maganin zazzabin cizon sauro.
Adan ka ga alamun kamuwa da zazzabin cizon sauro, yana da kyau kaje asbiti
mafi kusa domin a gwada agani ko ka kamu da zazzabin cizon sauro. Yanzu
asibitoci da yawa suna gudanar da gwaji nan take na zazzabin cizon sauro.
Kuma kana inya tsayawa ka karbi sakamakon gwajin nan take. I dan
sakamakon ya tabbatar ka kamu da zazzabin cizon sauro, to akwai bukatar
kayi maganinta da ACT domin kawar da karamin zazzabin cizon sauro kafin
ya zama mai tsanani.
4. menene ACT
Ana nufin hadin Antemasinin. Magunguna ne na musamman wadanda
gwamnatin Tarayyar Najeriya ta bayar da shawarar a gabatar ta kuma amince a
matsayin kyakkyawa kuma ingantaccen maganin zazzabin cizon sauro.
5. Menene muhimmancin amfani da ACT?
Bayan an shafe shakaru ana bincike cikin tsanaki a nan Najeriya da kuma
kasashe masu yawa, gwamatint Najeriya da kungiyoyin duniya da suka hada
da kungiyar nan ta Duniya (WHO) da Asibitin Tallafawa yara na Majalisar
dinkin duniya da sauransu suka gano cewa magunguna da dama da ada ake
amfani dasu wajen maganin zazzabin cizon sauro musamman ma kulorokwin
basa maganin zazzabin cizon sauro.
Zuzzurfan bincike ya kuma nun cewar idan aka hada Aitimisin a matsayin
sinadari mai karfi da wani maganin zazzabin cizon sauro, to wannan hadi na
sinadarin 2 masu karfi yana aiki sosai wajen maganin zazzabin cizon sauro.
Wannan ya fayyace dalilin daya sa gwamnatin Tarayyar Najerita da Kungiyar
Lafiya ta duniya da asusun tallafawa yara na majalisar dinkin duniya da sauran
kungiyoyin duniya suka amince da yin amfani da ACT a matsayin ingantaccen
maganin Zazzabin cizon sauro a dukkanin sassan najeri.
Akwai ACT Samfura 2 da aka amincewa (AA da AL)
6. wadanne ne alfanun ACT fiye da sauran magungunan zazzabin cizon sauro?
 ACT na kashe zazzabin Cizon Sauro fiye da sauran magungunan
zazzabin cizon sauro.
 ACT yafi sauran maganin zazzabin cizon sauro fiye da sauran
maganin zazzabin cizon sauro.
 Har yanzu dai ba a sami labarin inda ACT ya gaza kashe kwayar cutar
zazzabin cizon sauro ba a nan najeriya.
 Akwai wadatar Act kuma akan farashi mai sauki dan amfanin kowa.
7. Shin akwai wani hadari ne game da amfani da ACT?
 ACT nada kyau da inganci
 ACT na maganin matsayin da aka tabbatar an kamu da zazzabin cizon
sauro, a cikin kwana 3. Idan har bayan kwana biyu da amfani da ACT
ba’a ji sauki ba sai a je asibiti.
8. Shin a in azan sami ACT a garin mu kuma akan wane farashi?
 ACT na nan a asibitocin gwamnati da masu zaman kansu a kan farashi
mai sauki.
 Zaka iya samu ACT a asibitoci da manya da kananan Kantinan sayar da
magani da kuma masu tallan magani da kuma ma’aktar kula da lafiya na
kauyuka da unguwanni na sa kai.
9. Shin yaya zan yi amfani da ACT?
Ana yin Amfani da Maganin ACT bisa umarnin Likita ko jami’in kula da
lafiya ko kuma a bisa yadda ka’idarsa ke rubuce a jikin madaukin maganin
wato kwalin maganin.
 Yana muhimmanci yayin da ka fara amfani da ACT ya kasance ka cika
ka’idar kwanakin da aka baka koda ka daina jin alamun ciwon kafin
cikar wa’adin da aka baka.
 Idan ka yi amfani da ACT bisa ka’idar da aka shimfida

You might also like